Book Summaries

Learn key lessons from world-class books and apply them to your business and financial journey.

Published

SHA’AWA MAI ƘARFI SHI NE: MATAKIN FARKO NA CIMMA NASARA

Success Principles

By Napoleon Hill

Babban saƙon wannan sashi shi ne: fata kaɗai ba ta kawo nasara. Abin da ke kawo nasara shi ne sha’awa mai ƙarfi,da bayyana manufa,da tsari mai kyau, da fara aiki nan take. Idan mutum ya san ainihin abin da yake so,to ya rubuta shi,kuma ya sa lokaci, ya tsara abin da zai bayar a madadinsa, sannan ya dage.burinsa zai fi samun damar zama gaskiya.

Read Summary
Published

KA CIRE “BA ZAI YIWU BA” DAGA TUNANINKA

Wealth Mindset

By Napoleon Hill

Wannan sashi yana koyar da cewa babban abin da ke hana mutane ci gaba sau da yawa ba rashin kuɗi ba ne, amma irin tunanin da suke riƙe a zuciyarsu. Mutum da ya cika zuciyarsa da “ba zai yiwu ba,” “ba zan iya ba,” ko “ni ba irin waɗancan mutane ba ne,” yana rage damar da zai ga sabbin hanyoyi da dama. Darasin ya nuna cewa nasara tana farawa ne daga tunani mai manufa, imani da yiwuwar cimma buri, da ƙin karɓar gazawa a matsayin ƙarshe. An kawo misalin Henry Ford, wanda ya nace sai an ƙirƙiri injin V-8 duk da cewa injiniyoyinsa sun ce ba zai yiwu ba. Dagewarsa ta sa aka gano hanyar yin abin da wasu suka ɗauka ba zai yiwu ba.

Read Summary
Published

KADA KA TSAYA KUSA DA NASARA

Success Principles

By Napoleon Hill

Wannan sashi yana koyar da muhimmancin dagewa a lokacin da mutum ya fuskanci cikas. A aikin sa ko A kasuwancin sa. An kawo labarin R. U. Darby da danginsa da suka kusa samun zinariya, amma suka daina hakowa a lokacin da suka gaji da rashin sakamako. Daga baya, wani ya nemi shawarar ƙwararre, sai aka gano cewa zinariyar tana kusa sosai da inda suka tsaya. Darasin ya nuna cewa mutane da yawa suna barin buri ko business ɗinsu ne a lokacin da suke kusa da samun nasara. Wani lokaci matsala ba tana nufin ƙarshe ba ne; tana iya zama alama cewa mutum yana bukatar ƙarin ilimi, shawara, haƙuri, ko sabon tsari.

Read Summary